Home Kasashen Ketare Trump ya yi sassauci ga amininsa Rodger da kotu ta daure

Trump ya yi sassauci ga amininsa Rodger da kotu ta daure

109
0

Manyan ‘yan jam’iyyar dimokarat a kasar Amurka sun soma yin Allah wadai da wani mataki da shugaba Donald Trump ya dauka na rage hukunci da wata kotun kasar ta yi ga Roger Stone wanda amini ne ga shugaba Trump.

Kotun ta bayyana cewa ta yanke wa Roger Stone hukuncin makonni 40 a gidan yarin kasar ne bayan samun shi da laifin yin karya ga majalisa dama kawo mata cikas akan binciken da ta ke gudanarwa.

Elizabeth Warren, wata da ta taba fitowa neman tarakar shugabancin kasar a jam’iyyar ta dimokarat ta bayyana cewa a tarihin kasar ba a taba samun shugaba dan rashawa kamar Donald Trump ba.

Sai dai tuni masana a kasar ta Amurka suka fara bayyana cewa tsarin shari’ar kasar ya zama mai harshen-damo guda na shugaban kasa dayan kuma wanda ke aiki ga ‘yan kasa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply