Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi TSA: Gwamnatin Gombe ta gano bilyan 1.48 da asusun banki na rufa-rufa...

TSA: Gwamnatin Gombe ta gano bilyan 1.48 da asusun banki na rufa-rufa 265

105
0

Gwamnatin jihar Gombe ta ce ta bankado wasu kudi da suja kai darajar Naira bilyan 1.48 a wani binciken badakalar kudi da ake yi wa tsohuwar gwamnati.

Gwamnan jihar Inuwa Yahaya yace gwamnatin ta kuma gano asusun ajiya na banki da aka yi rufa-rufa da su guda 265.

Gwamna Inuwa Yahaya da ya ke bude taron bita na yini daya kan sabon tsarin asusun ajiya na bai daya “TSA” yace gwamnatin jihar ta shirya taron bitar ne ga jami’an sassan kudi da shugaban ma’aikatu da hukumomin gwamnati.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply