Rahotanni daga birnin Kano sun ce tsadar kayan masarufi ta sa an rufe gidan cin abincin nan da ake hada na Naira 30 a Kano.
Mamallakin gidan abincin, Alhaji Haruna Injiniya, ne ya tabbatar da hakan a wata ziyara da Freedom Radio ta kai masa.
Haruna Injiniya mazaunin Unguwar Sani Mai Nagge, ya ce tsadar kayan abinci ne ta sanya su rufe gidan, sabo da yanzu kudin kayan hadin ya ninka yadda ake saye a baya.
Ya ce duk da mutanen da ke zuwa cin abinci ba su ji dadin hakan ba, amma ala-tilas su rufe, ganin yadda komai ya yi tsada.
