Home Labarai Tsakanin 2018-2019 an kama masu bautar da yara 629

Tsakanin 2018-2019 an kama masu bautar da yara 629

98
0

Gwamnatin tarayya ta ce ta gurfanar da mutane 287 da kuma wasu 342 da ake zargi da bautar da yara a shekarar 2018 da 2019.

Ministan kwadago Chris Ngige ya bayyana a ranar Litinin, a Abuja, lokacin wani taron karawa juna sani da aka shirya wa ‘yan jarida, kan bada rahoton bautar da yara, da kuma gabatar da tsarin yaki da bautar da yara kanana a Nijeriya.

Ya ce ma’aikatar sa, ta karkashin ofishin karamin ministan Kwadago ta samu rahoton bautar da yara 5,401 da kuma 3,937, sannan an tallafa wa yara da iyalan wadanda suka fuskanci wannan matsalar su 1,494 da kuma 1,278 a shekarar 2018 da kuma 2019.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply