Kasar Jamus ta ce kimanin mutane 15,800 ne suka mutu sakamakon matsanancin zafin rana a wannan bazarar, yayin da wasu ƙasashen Turai ke fama da zafin rana da fari.
Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, cibiyar kiwon lafiyar ta Jamus (Robert Koch Institute – RKI) ce ta fitar da sabon rahoton a ranar Alhamis.
Rahoton ya nuna cewa mutanen da suka fi fuskantar haɗarin mutuwa sakamakon zafin rana su ne tsofaffi masu shekaru sama da 75.
RKI ta ce kusan mutane 9,600 sun mutu a cikin mako guda a ƙarshen watan Yuni, lokacin da yanayin zafi a wasu sassan Jamus ya haura digiri 40 na ma’aunin Celsius.
Bugu da ƙari, cibiyar ta ce an samu wasu mutane kusan 4,000 da suka mutu sakamakon zafin rana tsakanin ƙarshen watan Yuli zuwa tsakiyar watan Agusta.
Wannan adadin ya zarce na shekarar 2018, wadda a baya ce ke riƙe da tarihin mafi yawan mace-macen da ake dangantawa da zafin rana, inda aka samu kimanin mutane 8,900 da suka mutu.
Matsanancin zafi da fari sun addabi sassa da dama na Turai a wannan bazarar, lamarin da ya ƙara yawan mace-macen da ake dangantawa da zafi, tare da haddasa gobarar daji da lalata amfanin gona.
Haka kuma, matakan ruwa a wasu manyan kogunan Turai sun ragu sakamakon tsananin fari da zafin rana.
Masana sun ce matsanancin zafi na iya yin illa kai tsaye, amma a mafi yawan lokuta yana ƙara haɗarin mutuwa ga mutanen da ke fama da wasu matsalolin lafiya, musamman na zuciya, huhu ko ƙoda.
RKI ta bayyana cewa tana amfani da tsarin ƙididdiga wajen tantance mace-macen da zafi ya haddasa, ta hanyar kwatanta yawan mace-macen da ake samu a makonnin da ake fama da zafi da kuma makonnin da babu matsanancin zafi.
