Home Labarai Tsaro: Dattawan Arewa za su gana da gwamnonin Nijeriya

Tsaro: Dattawan Arewa za su gana da gwamnonin Nijeriya

21
0

Kungiyar Dattawan Arewa ta ce tana shiri gudanar da wani muhimmin taro da gwamnonin Kudu da Arewacin Nijeria domin tattauna yadda za a rage rudanin da ake fama da shi a kasar da kuma samar da kyakkyawar hanyar samun hadin kai da fahimtar juna a Nijeriya.

Kungiyar wadda ta yi kira ga jami’an tsaron yankuna da ke fadin kasar su dakatar da barazana da kai hare-haren da suke, ta kuma yi kira ga Fulani makiyaya masu biyayya ga doka da su dawo Arewa idan har suna ganin inda suke yanzu babu tsaro a tare da su.

Daraktan yada labaran kungiyar Dr. Hakeem Baba-Ahmad, wanda ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’ar nan a Abuja, bai fadi ranar da za a gudanar da taron ba, saidai ya yi kira ga Shugaba Buhari da gwamnonin kasar, su tuntubi juna tare da fito da matakan rage rudanin da ake ciki tare da ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa suna rayuwa a kasar da dokoki ke aiki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply