Home Labarai Tsaro: gwamna Matawalle ya gargaɗi sarakuna kan bada bayanan sirri

Tsaro: gwamna Matawalle ya gargaɗi sarakuna kan bada bayanan sirri

180
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya buƙaci sarakunan gargajiya su riƙa bada bayanan sirri ga jami’an tsaro don kawo ƙarshen ƴan bindiga, garkuwa da mutane da kuma satar shanu da yankin Arewacin Nijeriya ke fama da shi.

Gwamnan ya yi wannan kira ne ne a lokacin da ya tarbi jama’ar masarautun Shinkafi, Zurmi, Tsafe, Ƙaura Namoda, da Birnin Magaji da suka kawo masa ziyarar sallah a gidansa da ke Gusau.

Matawalle, ya ce sarakuna na da rawar da za su taka wajen samar da bayanan sirri ga jami’an tsaro wanda zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.

Da suke magana tun da farko, sarakunan yankunan sun nuna farin cikinsu kan yadda gwamnan ke tafiyar da harkokin tsaron jihar, sannan suka bada tabbacin ci gaba da mara masa baya a dukkan shirye-shiryensa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply