Home Labarai Tsaro: Gwamnatin Katsina na takaicin abin da ke faruwa-SGS

Tsaro: Gwamnatin Katsina na takaicin abin da ke faruwa-SGS

103
0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce tana takaicin abin da ke faruwa na dangane da matsalolin tsaro da wasu sassan jihar ke fuskanta a kwanakin nan.

Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Muhammad Inuwa ne ya furka haka a lokacin da ya amshi wata mata da ta samu kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane mai suna Hadiza Garba da sojoji suka ceto.

Mustapha Inuwa yace kada mutane su yanke kauna ga ayyukan da jami’an tsaro ke aiwatarwa, ganin yadda suke kai gwauro su kai mari domin tabbatar da sun kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar.

Sakataren gwamnatin ya umurci da a hannanta matar ga iyalanta bayan da ta shafe makonni 6 a hannun masu garkuwa da mutane.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply