Home Sabon Labari Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Masa’kar Samar da kayan Sarki

Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da Masa’kar Samar da kayan Sarki

93
0

Gwamnatin Tarayya ta ‘kaddamar da masa’kar Samar da kayan sarki na zamani domin biyan bu’katun Jami’an Tsaron Kasar nan.

Daraktan watsa labarai da kuma hulda da Jama’a, na Ma’aikatar Harkokin cikin Gida, Mista Mohammed Manga ya bayyana hakan a Abuja.

Mohammed Manga yace kaddamar da masakar me suna DICON-SUR Corporate Wears Nigeria Limited da ke Kakuri a Kaduna, zai magance yin amfani da Kayan sarki da ‘batagari suke yi wajan aikata munanan ayyuka.

Bugu da ‘kari Mista Manga yace masa’kar za ta samo auduga daga Jihohin Kaduna, Bauchi,Gombe, Katsina da dai sauran su.

Da yake jawabi Shugaban Kasa Muhammad Buhari Wanda ya samu wakilcin Ministan Harkokin cikin Gida Mallam Ogbeni Rauf Aregbesola yace Gwamnatin za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta kawo karshen duk wani matsalar tsaro da ya addabi Kasar nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply