Home Sabon Labari Tsaro: Ku yi koyi da Gwamnan Zamfara, Sarki ya shawarci Gwamnoni

Tsaro: Ku yi koyi da Gwamnan Zamfara, Sarki ya shawarci Gwamnoni

72
0

Saleem Ashiru Mahuta 

Sarkin Maradun da ke Jihar Zamfara a Arewa Maso Yammacin Nijeriya Garba Tambari ya shawarci gwamnonin yankin Arewa Maso Yammacin Kasar da su yi koyi da Zamfara kan samar da zaman lafiya da gwamnatin jihar ta bi domin kawo karshen matsalar ta’addanci a jihohin su.

Tambari wanda ya bayyana hakan sa’ilin da ya karɓi baƙuncin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa kan yadda za’a samar da matsugunnan fulani na zamani wato Ruga Settlement a ofishinsa a jiya Lahadi, ya ce hanyoyin da gwamnatin Gwamna Bello Matawalle ta ɓullo da su ya haifar da ɗa mai ido wajen samar da zaman lafiya a jihar.

Shi ma mai baiwa Gwamnan jihar shawara akan harkokin tsaro Abubakar Dauran ya bayyana wa Sarkin cewa, samar da matsugunnan fulani na zamani na daga cikin kokarin da gwamnatin Jihar ke yi wajen kawo zaman lafiya a dukkan wuraren da ake tashin hankuli, kuma nauyin da aka ɗorawa kwamitin shi ne binciko wuraren da za’a gina Rugagen Fulani a faɗin Jihar.

A cewar Dauran, kwamitin ya ziyarci dajin kauyen Rikwa da ke a yankin masarautar Ɗansadau na Karamar Hukumar Maru domin ganin yiwuwar fara shirin, yana mai cewa, an samu wurin da za’a aiwatar da shirin a yankin kamar yadda aka ba da shawarar samun kadada 20,000.

Yace karkashin shirin gwamnati za ta gina gidaje 500 masu ɗakunan kwana 2 da wajen kiwon dabbobi da ƙorama da makarantu domin karatun boko da na addini, da asibiti da asibin dabbobi da masallaci da kasuwar sayar da dabbobi da kuma ma’aikatar sarrafa madarar shanu, kuma dukkan su za’a gina ne domin fulanin da za’a tsugunar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply