Home Addini Tsaro: Kungiyar Izala ta umurci limamai su cigaba da adu’o’i na musamman

Tsaro: Kungiyar Izala ta umurci limamai su cigaba da adu’o’i na musamman

91
0

Shugaban kungiyar Izalah na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya umurci limaman da ke jagorantar salloli da su rika gudanar da “Alkunut” a cikin sallolinsu don neman Allah Ya kawo karshen ta’addanci a kasar nan.

Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi wannan kiran ne a shafukan kungiyar na sadarwa.

Ya yi kira ga musulmi da au tuba su daina sabon Allah, su kuma nemi yafiya bisa kura-kuran da suke aikatawa.

Idan za a tuna dai, ko a makon da ya gabata, limamai sun fara “Alkunut” domin neman dawowar zaman lafiya musamman a arewacin kasar nan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply