Home Sabon Labari Tsaro: Sarkin Katsina ya bukaci a yi doka don kawar da kidinafin

Tsaro: Sarkin Katsina ya bukaci a yi doka don kawar da kidinafin

86
0

Saleem Ashiru Mahuta/dkura

Mai Martaba Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir Usman ya yi kira ga yan majalisar dokokin jihar da su kafa dokokin da za su tabbatar da an hukunta dukkanin yan ta’adda da masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Sarkin na magana ne a yau Alhamis a yayin taron masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro wanda ya gudana a babban dakin taron sakatariyar gwamnatin jihar.

A cewar Sarkin rashin samar da dokokin a cikin al’umma na daya daga cikin dalilan da suka kawo yaduwar kashe kashe a jihar, yana mai kira ga wanda abun ya ta’allaka akan su da su tabbatar da ana bin dokokin da suka yi. Ya ce idan har aka bi dokokin sau da kafa ba tare da son rai ba, to za’a magance kashe kashen da ake yi wa mutane.

Abdulmumin ya kuma bukaci  yan Nijeriya su san mutanen da suke shigowa kasar, inda yayi kira akan yan siyasa da su guji taimaka wa yan ta’addan don cimma muradun su na siyasa, yana kuma mai kara kira ga Fulani da su cigaba da rike al’adun su da aka san su dasu domin a cewarsa fada da ta’addanci da kidinafin na bukatar hadin kan al’umma gaba daya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply