Home Labarai Tsaro: Shugaba Buhari zai bayyana gaban majalisa

Tsaro: Shugaba Buhari zai bayyana gaban majalisa

116
0

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya amince zai bayyana a zauren majalisar wakilai ta kasa don yi wa ‘yan kasa bayanin halin da ake ciki dangane da tsaro a kasar.

Shugaban majalisar wakilai Mr Femi Gbajabiamila ya sanar da hakan bayan ganawa da shugaban kasar a Abuja.

Gbajabiamila yace sun ziyarci fadar shugaban kasar ne domin bayyana masa matsayar majalisar na gayyatar da suka yi masa domin yi wa ‘yan kasa bayani dangane da tsaro.

Sai dai, yace ‘yan majalisar ba su saka ranar da shugaban kasar zai ziyarce su ba, amma sun ce nan ba da jimawa ba.

Radio Nigeria ta rawaito cewa babban makasudin gayyatar shugaban kasar shi ne ya yi wa ‘yan kasa bayanin halin tsaron da kasar ke ciki ta hannun wakillansu da ke majalisa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply