Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto ta shirya wata gasar rubutattun wakokin Hausa da za su yi magana akan karancin tsaro a Nijeriya.
Jami’ar dai a ta bakin shugaban kwamitin sadarwa na gasar Farfesa Salisu Ahmad Yakasai ya ce manufar shi ne bayar da dama ga marubuta wokokin Hausa don kawowa tare da nuni kan yadda za a magance matsalar tsaro a arewacin kasar.
Marubuta maza da Mata ne tsarin gasar ya ba dama don baje kolin basirar su.
Farfesa Yakasai yace za a kammala karbar wakokin a ranar 10 watan Fabrairu mai kamawa.
Kwararri, masana da alkalai ne za su tantance wadanda suka yi nasarar zama na 1 na 2 da kuma na 3, inda za su samu karramawa da kuma kyaututtuka yayin wani biki da za a shirya a jami’ar.
