Home Labarai Tsaro: ‘Yan bindiga sun hallaka Jami’an Kwastam biyu a jihar Neja.

Tsaro: ‘Yan bindiga sun hallaka Jami’an Kwastam biyu a jihar Neja.

80
0

Ahmadu Rabe

Hukumar hana fasa-kwauri ta Nijeriya shiyar jihar Neja ta tabbatar da kisan jami’anta guda biyu sakamakon harin ‘yan ta’adda.

Abba Yusuf Kasim wanda shi ne babban jami’in hukumar mai kula da shiyyar jihohin Neja da Kogi ya bayyana haka ya yin da ya ke zantawa da wakilin Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a garin Minna ta jihar Neja.

Abba ya bayyana cewa lamarin ya faru a ranar Alhamis da ta gabata 12 ga Disamba da misalin karfe 10:00 na dare ya yin da jami’an hukumar ke bakin aiki.

Ya kara da cewa harin ya yi sanadiyyar rasuwar jami’i Ohiremen S, mai mukamin Assistant Superintendent da kuma S.M. Omale da ke da matsayin Assistant Superintendent of Customs II.

Ya kuma ce akwai jami’in su daya da harsashin bindiga ya sama ya yin arangamar, wanda yanzu haka yana asibitin gwamnatin tarayya da ke garin Lokoja domin duba Lafiyar shi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply