Akalla mutane 147 aka tabbatar tsawa ta yi sanadiyar mutuwarsu a cikin kwanaki goma da suka gabata kasar Indiya.
Tuni dai masana kimiyya a fannin yanayi suka fara bayyana cewa hakan na faruwa ne sanadiyar dumamar yanayi.
Ita ma a nata bangaren ma’aikatar kula da yanayi ta kasar ta yi hasashen cewa za a iya fuskantar bala’o’i daban-daban sakamakon dumamar yanayi.
