Home Labarai Tsoho mai shekaru 72 da ake zargin ya yi wa ‘diyarsa ciki...

Tsoho mai shekaru 72 da ake zargin ya yi wa ‘diyarsa ciki a Gombe

72
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”g2uonvbhl” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”m16zsduby” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”m1ncvp3bra” animation_delay=”0″]

Alkalin kotun majsitare ta 10 a Gombe ya bayar da umarni a ranar Litinin din nan cewa a garkame Ibrahim Yunusa mai shekaru 72 da haihuwa. Ana dai zargin tsohon da yi wa diyarsa ta cikinsa fyade da kuma yi mata ciki.

Tun da farko a lokacin da  Dalaky Wanma, mai gabatar da kara ke yiwa kotu bayani, ya zargi tsohon da aikata wadannan laifuka a lokuta daban daban a tsakanin Disambar  2018 zuwa watan Janairu na 2019.

Mr. Dalaky yayi zargin cewa Ibrahim Yunusa yayi jima’i da diyarsa ta cikinsa mai shekaru 17 ba tare da son ranta ba.  Abin da daga karshe ya haifar mata da samun juna biyu. Ya ce an kuma aikata laifin a cikin gidan shi wanda ake zargin. Mai gabatar da karar ya ce wannan ya saba wa sashe na 390 da sashe na 282 na dokar Penal code.

Sai dai Ibrahim Yunusa mazaunin Karamar Hukumar Yamaltu Deba ta jihar Gombe ya musanta aikata wadannan laifuka.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya-NAN- ya ce mai gabatar da kara na ‘yan sanda Sgt. Bako Shekari ya shaida wa kotun cewa ‘yan sanda sun fara bincike akan lamarin. A don haka ya bukaci kotu da ta d’age sauraran karar domin ‘yan sanda su sami damar gudanar da cikakken bincike kuma a samu shawara ta shari’a daga ma’aikatar shari’a.

Alkalin kotun, Daura Sikkam, ya yarda da wannan bukata inda ya dage karar har zuwa ranar 13 ga watan Nuwamba mai zuwa.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply