Akalla mutane takwas aka tabbatar da mutuwarsu sannan gidaje 25 sun kone kurmus a sanadiyyar fashewar iskar gas a Legas.
Darakta-Janar na Hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu, ya tabbatar faruwar lamarin.
Fashewar ta auku ne a yankin Baruwa da ke karamar hukumar Alimosho da misalin karfe 5:45 na yamma a wajen wani wurin sayar da abinci.
