Ɗan takarar shugabancin Amirka na Jam’iyyar Democrats Joe Biden ya ce shi tuni ya fara shirin aiki a matsayin shugaban ƙasa.
A bayanin da ya yi ranar Juma’a a Wilmington na jihar Delware, Biden, ya ce yana da tabbacin shi zai ci zaɓen duk da ba a gama ƙidaya ƙuri’u ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya ce tuni sun fara tuntubar ƙwararru kan shirin komawa White House, shi da mataimakinsa Kamal Harris.
A daidai lokacin da yake jawabin dai, Biden yana ƙara ba shugaba Donald Trump rata a jihohin Arizona, Georgia, Nevada da Pennsylvania, waɗanda da farko Trump ke jagorantar nasara a cikinsu.
