Home Kasashen Ketare Twitter ya dakatar da Trump na har abada

Twitter ya dakatar da Trump na har abada

120
0

Kamfanin Twitter ya dakatar da adireshin shugaban ƙasar Amirka Donald Trump na dindindin a ranar Juma’a saboda kaucewa kalaman tunzura jama’a.

Twitter sun ce da farko an dakatar da Trump ne na sa’o’i 12 a ranar 6 ga watan Janairu saboda kalaman tunzura jama’a masu haɗari da ya yi, na yin tir da mataimakinsa Mike Pence, daidai lokacin da magoya bayansa suka hari Capitol.

Kamfanin ya ce “bayan bitar saƙonnin da ke fitowa daga adireshin @realDonaldTrump da kuma abubuwan da sakon ya ƙunsa, mun dakatar da shi na har abada saboda kaucewa kalaman da za su janyo rikici”.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply