Home Kasashen Ketare UAE ta tsawaita dakatar da safara daga Nijeriya zuwa Dubai

UAE ta tsawaita dakatar da safara daga Nijeriya zuwa Dubai

18
0

Hadaddiyar Daular Larabawa ta tsawaita hana safarar jiragen sama daga Nijeriya musamman Lagos da Abuja zuwa Dubai, daga ranar 28 ga watan Fubrairu zuwa 10 ga watan Maris.

Ma’aikatar sufurin saman kasar ta bayyana haka a cikin bayanan da ta wallafa a shafin intanet na kamfanin jirgin saman Emirates mallakin kasar.

Sanarwar ta ce an yi dakatarwar wucin gadi na daukar fasinjoji daga Lagos da Abuja zuwa Dubai daga nan zuwa 10 ga watan Maris bisa umurnin gwamnatin kasar.

Kamfanin Emirates dai ya dakatar da safararsa zuwa Nijeriya kwanaki kadan bayan gwamnatin tarayya ta dakatar da ayyukan kamfanin saboda shigo da tsarin gwajin Covid-19 ga fasinjoji masu zuwa Dubai, wanda ya saba da tsarin da ake amfanin da shi a Nijeriya.

Duk da cewa gwamnati ta janye hukuncin da ta sanya wa kamfanin biyo bayan sanarwar da kamfanin ya yi na janye tsarin da gwajin da ya zo da shi, har yanzu Emirates bai dawo da safarar fasinjoji ba daga Nijeriya zuwa Dubai, saidai duk da haka yana aikin sa na dauko fasinjoji daga Dubai zuwa Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply