Home Kasashen Ketare Uganda ta sa ranar zaben shugaban kasa

Uganda ta sa ranar zaben shugaban kasa

73
0

Hukumar zabe a kasar Uganda ta bayar da sanarwar cewa za ta gudanar da zaben shugaban kasa a tsakanin watan Janairu zuwa watan Fabrairu na shekara mai zuwa.

Simon Mugenyi Byabakama wanda shi ne Shugaban hukumar zaben kasar ta Uganda ya bayyana haka. Ya kuma ce za’a dauki matakan kariya domin kauce wa bazuwar annobar coronavirus a lokacin zaben.

Sai dai kuma hukumar ba ta kai ga bayyana takamaimai ranakun da za a gudanar da zaben ba.

Sanarwar da hukumar ta bayar, ta biyo bayan zargin da ‘yan adawar kasar ke yi na cewa Shugaba mai ci Yoweri Museveni na son fakewa da coronavirus domin dage zaben kasar duk da dadewarsa fiye da shekaru 30 a kan mulki

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply