Home Kasashen Ketare UNICEF: an haifi jarirai milyan 29 a lokuttan rikice-rikice a shekarar 2018

UNICEF: an haifi jarirai milyan 29 a lokuttan rikice-rikice a shekarar 2018

71
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”f79606wu2f” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”qjka5sucr” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”2hy6jcq7p8″ animation_delay=”0″]

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce sama da jarirai milyan 29 ne aka haifa a wuraren da ake rikice-rikice a shekarar bara, 2018.

 

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa daya daga cikin jarirai biyar da ake haihuwa na fara rayuwarsu ne a wuraren da ke da hatsari a duniya. Rahoton ya ce kasashen da lamarin ya fi kamari su ne na Afghanistan, Somalia, Sudan Ta Kudu, Syria da Yemen.

 

A cikin wata takarda da shugabar Asusun na UNICEF  Henrietta Fore ta fitar, ta ce akwai  miliyoyin iyalai da ba su samun abinci mai gina jiki, tsaftataccen ruwan sha, da wuraren zama masu tsafta. Mrs Henrietta ta ce rashin wadannan ababen more rayuwa na kawo cikas ga rayuwar kananan yara.

 

A cikin takardar, ta ce wani ma’aikacin asusun UNICEF a kasar Yemen ya ga kananan yara na fama da tamowa da sauran matsalolin da ke kawo wa rayuwar yara tarnaki ta dalilin tashin rikice-rikice. Sai asusun na UNICEF ya ce iyayen da ke tsugune a wuraren da ake rikice-rikice na matukar bukatar tallafi da su da yaransu.

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply