Home Labarai UNICEF ta mayar da yara miliyan 1.3 makaranta a arewacin Nijeriya

UNICEF ta mayar da yara miliyan 1.3 makaranta a arewacin Nijeriya

99
0

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yi sanadiyyar mayar da yara sama da milyan 1.3 makaranta a jihohi shida da ke Arewacin Nijeriya ƙarƙashin shirinsa na tallafa wa ilimi.

Jami’ar asusun mai kula da sashen ilimi Mrs Azuka Menkiti ce ta bayyana hakan ya yin da ta ke jawabi a wani taro na yini biyu da UNICEF ta shirya a Abuja.

Ta ce karamin ministan ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, ya gamsu da duk shawarwarin da aka bayar, sannan ya yi kira ga gwamnatoci a dukkan matakai kan buƙatar da ke akwai ta shawo kan yadda yara ke kaurace wa zuwa makarantu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply