Asusun yara na majalisar ɗinkin Duniya UNICEF ya ƙudiri aniyar sanya yara mata milyan 1 a makarantun firamare da ma na allo a jihohi shida na arewacin Nijeriya, a shirin da yake na taimakawa ilimin mata kashi na uku.
Jami’in kula da ilimi na UNICEF, Mista Saka Adebayo Ibraheem ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Katsina, yayin ganawa da wakilan kwamitin gudanarwar aikin.
Kazalika asusun ya tabbatar da sanya Ƴaƴa maza kusan milyan 2 a makarantun, da ma ɓullo da hanyar da za a inganta ƙwarewar malamai da tsarin tafiyar da makarantu a jihohin Katsina, Zamfara, Kano, Sokoto, Bauchi da Neja.
