Home Sabon Labari An sace jaririn kwanaki uku a Kaduna

An sace jaririn kwanaki uku a Kaduna

93
0

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ce tayi nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargi da satar wani yaro dan kwanaki uku da haihuwa a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mohammed Jalige, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Kaduna. Jaridar DCL Hausa ta samu rahotan cewa tun kafin mahaifiyar jaririn ta haihuwa wadanda ake zargin suka kulla kawance da ita domin su aikata abin da ake zargin su da shi a yanzu.

Mista Jalige ya ce a ranar 9 ga Nuwamban nan ne jami’an rundunar suka karbi korafin satar yaron dan kwanaki uku.

Ya bayyana cewa bayan da suka samu korafin, sai jami’an rundunar suka fara aiki nan take, inda suka ci gaba da tattara bayanan sirri sannan suka samu nasarar cafke wadanda ake zargin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply