Home Labarai Waɗanda aka sace a Kagara suna dajin Birnin Gwari – Matawalle

Waɗanda aka sace a Kagara suna dajin Birnin Gwari – Matawalle

28
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce waɗanda suka sace malamai da ɗaliban Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kagara, sun aje su ne a dajin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Gwamnan wanda ya bayyana haka a wani shirin talabijin a ranar Lahadi, ya ce nan ba da jimawa ba za a saki waɗanda aka sacen.

Matawalle ya kuma yi kiran samun haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki, yana mai cewa wannan ne babban matakin samun nasara a yaƙin da ƙasar je yi da ayyukan ta’addanci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply