Home Labarai Waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jigawa sun koka

Waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jigawa sun koka

141
0

Ɗaruruwan waɗanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su ne a ƙaramar hukumar Haɗejia da ke jihar Jigawa ne, ke koka wa kan mawuyacin halin da suka tsinci kansu a cibiyoyin da aka tsugunar da su.

Solacebase ta ruwaito cewa mutanen, waɗanda aka tsugunar a cibiyoyi 13 a cikin ƙaramar hukumar, sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta yi watsi da su, da kuma yadda yunwa da sauran cutuka ke damunsu.

Wata sanarwa da shugabar gidauniyar tallafa wa mata da marayu Malama Fatima Kaila, ta fitar a Haɗejia, ta ce gwamnati ta nuna halin ko in kula ga mutanen, tun bayan da ambaliyar ruwan ta raba su da gidajensu.

Ta kuma yi kira ga gwamnatin da sauran masu ruwa da tsaki, su tausaya wa mutanen, tana mai cewa tsananin da suke ciki ya sanya wasu sun fara barin matsugunnan saboda wahala.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply