Home Labarai Wadanda suka kamu da coronavirus a Turai ya haura dubu 200

Wadanda suka kamu da coronavirus a Turai ya haura dubu 200

83
0

Sama da mutane 200,000 ne suka kamu da cutar coronavirus a nahiyar Turai, inda kasar Italiya ke da 63,927, Sifaniyaa 39,673, da ya sanya suke da sama da rabin adadin wadanda suka kamu da cutar a nahiyar, kamar yadda rahoton AFP na ranar Talata ya nuna.

Wannan adadi na 200,000 da suka kamu da cutar, da kuma mutum 10,732 da suka mutu, ya sa nahiyar ta zama inda cutar ta fi yin ta’adi, sai Nahiyar Asia ke biye mata inda mutum 98,748 suka kamu, kuma 3,570 suka mutu.

Wannan cuta dai ta fara barkewa ne a kasar China cikin watan Disambar bara.

Rahotanni dai sun nuna wannan adadi na wakiltar kusan rabin wadanda suka kamu da cutar ne a kasashe da dama, a daidai lokacin da wadanda aka kawo a asibiti ne kadai ake yiwa gwajin cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply