Home Labarai WAEC: Atiku ya caccaki gwamnati

WAEC: Atiku ya caccaki gwamnati

215
0

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce hana daliban sakandare su zana jarabawar karshe ta WAEC zai jefa Nijeriya cikin hadari.

Atiku ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, yace a matsayinsa na mahaifi, ya kamata a ce gwamnati ta dauki matakin da yara za su samu damar zana jarabawarsu kada shekarar ta wuce a haka.

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace yin hakan zai maiyar da su baya. Ya kara da cewa sam wannan mataki da aka dauka bai kamata ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply