Gwamnatin jihar Gombe ta ce dalibai bakwai da ke rubuta jarabawar karshe a makarantar sakandaren mata ta gwamnati a garin Doma sun kamu da cutar corona.
Kwamishinan Ilimi na jihar, Dokta Habu Dahiru, ne ya bayyana hakan ya yin da ya ziyarci daliban a ranar Larabar makon nan.
