Home Labarai WAEC: Har yanzu gwamnati na kan bakanta

WAEC: Har yanzu gwamnati na kan bakanta

155
0

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa har yanzu tana nan akan bakanta na hana daliban sakandare zana jarabawar su ta karshe wato WAEC.

Karamin minista a ilimi Chukwuemeka Nwajiuba ya bayyana haka ya yin zantawar sa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa na mako-mako da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta.

Sai dai ya ce hukumar shirya jarabawar ta WAEC ta fara tattaunawa da kasashen yammacin Afirka game da yiyuwar dage ranakun rubuta jarabawar har sai yadda hali ya yi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply