Home Coronavirus WAEC: Nijeriya ta damu da yadda wasu dalibai suka kamu da corona

WAEC: Nijeriya ta damu da yadda wasu dalibai suka kamu da corona

117
0

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta damu matuka da yadda aka samu wasu dalibai da ke zauna jarabawar karshe ta ‘yan sakandare WAEC sun harbu da cutar corona.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya nuna damuwar a lokacin taron kwamitin yaki da cutar corona na kasa karo na 59 a Abuja.

Ya ce akwai bukatar a kara hankalta, musamman a sashen ilmi da yanzu ake zauna jarabawar karshe ta daliban sakandare a nahiyar Afrika ta yamma.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply