Home Sabon Labari Wane ne Marigayi Aminu Manu na Rediyo Faransa?-El-Hikaya

Wane ne Marigayi Aminu Manu na Rediyo Faransa?-El-Hikaya

121
0

Nasiru Adamu El Hikaya dan jarida, wakilin gidan rediyon VOA a Abuja ya rubuta cikakken bayani na yadda rayuwar aikin Marigayi Aminu Manu (wakilin rediyon Rfi Hausa a Abuja) wanda ya rasu a ranar 28.10.2019 ta kasance.

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN-ALLAH YA JIKAN AMINU AHMAD MANU NA REDIYON FARANSA DA RAHAMA.
Makwanni 3 da su ka wuce ina shirin tafiya Gombe don ta’aziyyar rasuwar suruki na Malam Ahmad Usman sai na ga wayar Aminu na dauka ina tsammanin ya na Jos ne ya bugo don mu gaisa kasancewar ya na jinyar ciwon suga a asibitin JAN KWANO. “ka na ofis ne?” ya tambaye ni na ce na dan fita amma zan dawo ba da dadewa ba.Ashe ya shigo Abuja bayan samun sauki.Haka a ka yi na dawo ofis ya zo mu ka dade mu na hira.Na ba shi shawarin ya dakata da tuka mota. Cikin hirar mu ya ce duk wadanda su ka kwanta da su a asibiti sun riga mu gidan gaskiya sai shi Allah ya raya zuwa wannan lokaci.Allah Akbar! saukin na komawa ga mahalicci ne.
Daga 2007 da Bashir Ibrahim Idris ya dawo da Aminu Manu Abuja don yi wa rediyon Faransa aiki,mu ke aiki tare da shi duk da dama ina hulda da shi tun ya na Jos. A ofishi na ya fi zama kuma ya kan kira ni da “NAS” a takaice.A ‘yan shekaru 2 zuwa 3 a baya, ya rage aikin jarida na kai tsaye in ba fitowa a shirye-shirye kamar IDON MIKIYA na Vision FM da Farin wata ba. A gamuwar mu da shi ta karshe ya ce zai nemi wani aiki a majalisar dokoki da ba zai rika jigilar da za ta wahalar da jikin sa ba don yanayin lafiyar sa. Don ba shakka aikin jarida kan dauke hankalin mutum ya kasa ko zuwa asibiti in ba ciwo ya kwantar da mutum ba ga kuma dogon nazarin yadda za a fito da labaru masu ma’ana. Aminu kan shigo a gajiye wani lokacin ya ce min “NAS AN BA NI LABARIN MINTI DAYA DA RABI” bisa ma’ana aikin fito da labari a jawabai da za su iya kai wa minti 60 ko ma 90 amma a minti daya da rabi. Nan take na kan ce ai ba komai za ka iya. Akwai wasu daga irin rahotannin na Manu a na’ura ta mai kwakwalwa.
Wanda ya san marigayin,zai fahimci mutum ne wanda ba ya boye abun da ya ke ran sa,kuma da zarar ya yi magana shikenan komai ya wuce.Hakika an yi rashin masoyin al’ummar arewacin Najeriya.
ALLAH YA JIKAN SA DA RAHAMA.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply