Wani Ba’amuriken ɗan mishan mai suna Kevin Rideout ya shaƙi iskar ‘yanci bayan shafe sama da watanni tara a hannun masu garkuwa da mutane a Nijar, kamar yadda ƙungiyar SIM International da yake yi wa aiki ta tabbatar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an sace Rideout ne a watan Oktoban 2025 a wajen gidansa da ke birnin Yamai, babban birnin Nijar, inda wasu mutane uku ɗauke da makamai suka yi awon gaba da shi.
Rahotanni sun ce masu garkuwar sun kai shi yankin Tillaberi da ke yammacin Nijar, wanda ya dade yana fuskantar hare-haren ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
A cikin wata sanarwa da SIM International ta fitar ranar Juma’a, ƙungiyar ta ce Rideout yana cikin ƙoshin lafiya kuma a halin yanzu yana ƙarƙashin kulawar jami’an Amurka.
Jaridar The New York Times, wadda ta fara bayar da rahoton sakin nasa, ta nakalto wasu jami’an Amurka da ba a bayyana sunayensu ba suna cewa Rideout yana hannun FBI.
Sai dai har yanzu ba a bayyana yadda aka samu nasarar kuɓutar da shi ko kuma waɗanda suka riƙe shi ba.
Tun bayan sace shi ne aka fara nuna damuwa kan yiwuwar cewa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ne suka yi garkuwa da shi, ciki har da Al-Qaeda da ke aiki a yankin Sahel.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya kuma ruwaitocewa bisa bayanan majiyoyin diflomasiyya, mutane uku ɗauke da makamai ne suka yi awon gaba da Rideout zuwa yankin Tillaberi.
Rideout ya shafe shekara 19 yana aikin da’awa da taimakon al’umma a Nijar.
Baya ga aikin mishan, ya kasance matukin jirgin sama da ke aiki da SIM International, ƙungiyar da ke gudanar da ayyuka a sama da ƙasashe 70 na duniya.
SIM International ta bayyana sakin nasa a matsayin “labari mai matuƙar faranta rai”, bayan watanni da aka shafe cikin rashin tabbas game da lafiyarsa da inda yake.
Ƙungiyar ta ce Rideout zai sake haɗuwa da matarsa, ‘ya’yansa da sauran ‘yan uwansa bayan dogon lokaci da suka shafe ba tare da shi ba.
