Home Labarai Wani abin fashewa ya kashe mutane 7 a Katsina

Wani abin fashewa ya kashe mutane 7 a Katsina

377
0

Wani abin fashewa ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 7 karin wasu 6 suka jikkata a kauyen ‘Yammama na karamar hukumar Malumfashi jihar Katsina.
Rahotannin DCL Hausa ta tattaro na cewa abin fashewar ya dargwaje ne a yayin da wadannan yara suka je dibar abincin dabbobi a bayan gari.
A baya-bayan nan dama wasu na zargin cewa Boko Haram ta yi nasarar hadewa da ‘yan bindigar jihohin Katsina da Zamfara. Sai dai DW Hausa ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Isah Gambo na cewa ‘yan sanda na ci gaba da bincike a kan lamari.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply