Home Coronavirus Wani kwamashinan ‘yansanda ya mutu

Wani kwamashinan ‘yansanda ya mutu

313
0

kwamishinan ‘yansanda na jihar Cross River, Abdulkadir Jimoh ya mutu.

Jaridar Blueprint ta rawaito cewa akwai alamu cewa corona ce ta yi ajalin Jimoh bayan da alamominta suka bayyana a jikinsa kafin ya mutu.

Babban Likita a asibitin koyarwa na Jami’ar Calabar, UCTH, Farfesa Ikpeme Ikpeme, ya tabbatar da labarin mutuwar Jimoh din a ranar Juma’ar nan, inda ya ce an kawo marigayin zuwa asibitin bayan ya riga ya mutu.

Ya kuma shawarci duk waɗanda suke tare da shi da su ziyarci asibiti don gwajin corona kuma daga baya su kasance cikin keɓe kai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply