Home Lafiya Wanke Baki: MASANA SUN CE A KOMA GA ASUWAKI

Wanke Baki: MASANA SUN CE A KOMA GA ASUWAKI

116
0

Wani masani akan muhalli a kasar Ghana ya shaidawa Sashen Turanci na DW cewa idan mutanen kasashen Afrika su na amfani da buroshin-wanke-baki guda biyu a shekara daya, to hakan na nufin akalla Bilyan Biyu da Milyan Dari Hudu (2.4 Billion plastic brushes) na buroshin roba(brush) ne ake jefarwa wadanda a karshe ke shiga rafuka da kogi na wannan nahiya tamu.

A saboda haka wannan masanin da wasu abokan aikinsa suka fito da shawarar kira ga jama’a su koma wanke baki da itatuwa watau Asuwaki (abin da addinin musulumci ya bukata)

Zullumin masanan dai shi ne samun Bilyan Biyu da Milyan Dari Hudu (2.4 Billion plastic brushes) na buroshin roba na fadawa cikin rafi da kogi da koramun Afrika toh hakan ka iya kassara sanaar noma da kiwon kifi a saboda yadda robobi na plastic ke cutar da muhalli

Shin da me kuke wanki baki? Za ku iya komawa amfani da asuwaki a maimakon burushi na roba?

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply