Home Coronavirus Wasan zari-ruga: Usain Bolt ya kamu da corona

Wasan zari-ruga: Usain Bolt ya kamu da corona

127
0

Dan wasan tseren zari-ruga dan asalin kasar Jamaica, Usain Bolt, ya harbu da cutar corona.

Bolt wanda shi ne ya sanar da haka a shafinsa na twitter, yace yanzu haka ya killace kansa a inda ake kula da masu cutar corona.

A ranar Juma’ar makon da ya gabata, Usain Bolt ya yi bikin cika shekaru 34 da haihuwa.

Rahotonni sun ce, dan wasan Manchester City Raheem Sterling tare da dan wasan gefen kungiyar Bayern Leverkusen sun halarci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Bolt din.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply