Home Kasashen Ketare Wasanni: Ina son Arsenal su kara hakuri da Emery-Henry.

Wasanni: Ina son Arsenal su kara hakuri da Emery-Henry.

87
0

Ahmadu Rabe

Tsohon kyaftin din Arsenal Thierry Henry ya wallafa ra’ayinsa a shafinsa na kafar sadarwa cewar kamata ya yi tsohuwar kungiyar ta sa ta manta da batun lashe kofin gasar Firimiya, ta kara yin azama wajen ganin ta kammala wasannin ta cikin kungiyoyi ‘yan hudun farko domin samun tikitin shiga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a kaka mai zuwa.

Henry ya kuma bukaci magoya bayan kungiyar da su kara bai wa kocin kungiyar Unai Emery lokaci domin samun isasshen lokacin da zai kara saita kungiyar ta dawo kan ganiyarta.

Tun a kakar wasa ta shekarar 2015/16 Arsenal din ba ta kara samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar zakarun turai ba sai a Wannan kakar.

kungiyar dai ko a baya-bayan nan ta rika yin rashin nasara a wasannin ta, ciki hada wasan da ta buga da kungiyar Bayern Munich inda suka yi rashin nasara wasan gida da waje da ci 10 – 2 jimilla.

Maki daya ne ya hana ta zuwa gasar a bara, amma kuma Manchester City da ta lashe gasar Firimiyar ta Ingila a kakar ta ba ta ratar maki 28.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply