Home Sabon Labari Wasanni: Man United za ta kece raini da Wolves

Wasanni: Man United za ta kece raini da Wolves

62
0

Daga: Ahmadu Rabe Yanduna/NIB

A yau Litinin za a kawo ƙarshen wasannin mako na biyu a ci gaba da gasar firimiya lig ta ƙasar Ingila, inda Wolverhampton za ta karɓi baƙuncin Manchester United a filin wasa na Molineux.

Ƙungiyar Wolves dai na da maki ɗaya ne kacal bayan ta yi canjaras da Leicester City a wasan farko.

United kuwa, ta haɗa maki uku ne a wasan farko na kakar bana, bayan da ta lallasa Chelsea da ci 4-0.

A kakar bara, United ta kasa doke Wolves a haɗuwa biyu da suka yi, inda ta yi rashin nasara a gidan Wolves da ci 2-1 sannan suka tashi 1-1 a Old Trafford.

Sannan a ranar 16 ga watan Maris, 2019 ƙungiyar Wolverhampton ce ta fitar da United a gasar cin kofin ƙalubale na FA.

Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce ya san cewa Wolveshampton wadda Nuno Espirito Santo ke jagoranta ƙungiya ce mai tsauri, amma duk da haka zai saka ƙaimi don samun maki uku ringis a kan su.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply