Home Kasashen Ketare Wasanni: Manchester United ta taka wa Liverpool Burki.

Wasanni: Manchester United ta taka wa Liverpool Burki.

74
0

Ahmadu Rabe/Jani

Kungiyar Liverpool ta gamu da cikas bayan yin chanjaras a wasan su da Manchester United wasan mako na 9 a gasar Firimiyar kasar Ingila, inda aka tashi wasa kwallo daya da daya (1-1).

Rashin nasarar da Liverpool din ta yi a hannun Manchester United, ya hana kungiyar kafa tarihin buga wasanni 18 a jere ba tare da an yi nasara a kansu ba, kamar yadda kulob din Manchester City ta kafa a kakar shekarar 2017/2018.

Haka kuma rashin nasarar ya kara rage tazarar da ke tsakanin Liverpool da Manchester City zuwa maki 6 daga 8, Liverpool din na ci gaba da rike kambunta a matsayin jagora a gasar ta firimiya da maki 25.

Kocin kungiyar ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce Manchester United kan shirya tsaf a duk lokacin da za su fafata da Liverpool don kaurace wa shan kaye.

Jurgen Klopp ya kara da cewa ba komi United din suka yi a wasan na jiya ba, face tsare gida tare da hana ‘yan wasan Liverpool su kai masu farmaki.

Da wannan sakamakon Manchester United ta koma mataki na 13 da maki 10 kacal kuma maki 2 Kwal tsakanin ta da yan dagaji wato (relegation), Shekaru 5 kenan dai rabon da Liverpool ta yi nasara akan Manchester United a gasar ta Firimiya.

Yanzu dai an fara hasashen nasarar da Manchester United ta yi za ta iya tabbatar da Solkjear ya ci gaba da horas da kungiyar wanda da ake rade-radin zai iya rasa aikin horas da kungiyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply