Home Labarai Wasanni: muhimman abubuwan da suka gudana a gasar firimiya mako na 8

Wasanni: muhimman abubuwan da suka gudana a gasar firimiya mako na 8

86
0

Ahmadu Rabe/Jani

Ya yin da ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin gasar firimiya lig, an kammala wasannin mako na Takwas, sai dai wannan makon ya zo da sabon salo inda wasu daga cikin manyan kungiyoyi da dama suka sha mamaki.

Manchester City ta yi rashin nasara a filin wasanta na Etihad, inda kulob din Wolves ya sha su da ci 2-0.

City dai na fama da matsalar masu tsaron baya ya yin da mafi akasarin su ke jinya. Ko a makon da ya gabata, dan wasan tsakiyar kungiyar, Kevin De Bruyne ya samu rauni a kafarsa.

Ita ma Man United ta ziyarci kungiyar Newcastle inda aka masu ci daya mai ban haushi 1-0

Brighton sun karbi bakuncin Tottenham sun kuma kunya ta su da ci 3-0.

Kungiyar Arsenal da Chelsea sun fara farfado da darajarsu, inda duk suka ci wasan su a wannan makon.

Chelsea ta zazzaga kwallaye hudu rigis a ragar Southampton.

Maki uku da Arsenal ta samu akan kungiyar Bournemouth ya ba ta damar zama a matsayi na uku a teburin gasar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply