Daga Saleem Ashiru Mahuta
Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Paul Pogba ya kammala shirinsa na barin kungiyar a kakar musayar ‘yan wasan bana duba da sha’awar da Real Madrid ta nuna a kansa.
Dan asalin kasar Faransa wanda Zinedine Zidane ya bayyana bukatarsa a fili a farkon musayar ‘yan wasan, inda kuma ake ganin akwai alamun samun nasara akan wannan kudirin nasa.

Rahotanni na nuni da cewar United ta sa Euro Miliyan 150 a matsayin farashin dan wasan Wanda ta karya tarihin kudin sayen dan wasan, inda aka so a saye shi akan Euro Miliyan 89 a shekarar 2016.
Ya zuwa yanzu kungiyar kwallon kafar Real Madrid ta kashe Euro Miliyan 275 a kakar wasan bana, inda kuma ake sa ran za a samu karin wasu idan har ta gama sanya hannu a yarjejeniya da dan wasa Neymar, duk da ana ganin kamar da wuya Real din ta iya sayensa daga Old Trafford din.
