Home Labarai Kwallon Kafa: Rodrygo ya yi abin a zo a gani a...

Kwallon Kafa: Rodrygo ya yi abin a zo a gani a karawarsu da Galatassary

73
0

Dan wasan Real Madrid dan asalin kasar Brazil Rodrygo ya taka muhimmiyar rawa a wasan da Real Madrid ta lallasa Galatasary da ci shida (6) da nema (0) inda ya samu damar cin kwallo ukku 3 rigis.

Rodrygo mai shekara 18, shi ne dan wasa na biyu mafi kankantar shekaru da ya ci kwallo uku rigis a gasar Champions League bayan Raul Gonzalez.

Da Wannan Bajinta har an fara masa lakabi da “sabon Neymar” ganin yadda ya koma kasar Sifaniya da taka-leda daga kungiyar Santos ta Brazil kamar yadda Neymar ya yi – zuwa Barcelona a shekarar 2013.

“Daga sanda na ji an fara rera sunana a Bernabeu na san cewa mafarkina ya zama gaskiya,” in ji Rodrygo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply