Home Kasashen Ketare Wasanni: Sai Disamba Pogba zai dawo Atisaye- Solskjaer

Wasanni: Sai Disamba Pogba zai dawo Atisaye- Solskjaer

90
0

Ahmadu Rabe/Jani

Mai horas da kungiyar Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce dan wasan tsakiyar kungiyar dan asalin kasar Faransa Paul Pogba ba zai dawo fagen tamaula ba har sai watan Disamba.

Bayan yin hutunsa a Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, don samun cikakken lokacin murmurewa, kocinsa ya ce har yanzu zai iya kara zaman wata daya ba tare da ya murza leda ba.

Manchester United sun buga wasa a ranar Lahadi kuma sun taka rawar gani a wasan da ta yi da Norwich ba tare da Pogban ba, inda kungiyar ta yi nasara da ci 3-1, lamarin da ya sa ta kawo karshen wasanni 4 a jere ba tare da yin nasara ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply