Home Labarai Wasanni: Tottenham Na Zawarcin Mourinho

Wasanni: Tottenham Na Zawarcin Mourinho

95
0

Ahmadu Rabe/Jani

Kulob din Tottenham na kasar Ingila ya soma tuntubar Jose Mourinho, tsohon kocin Manchester United da Real Madrid kan yiwuwar karbar ragamar horas da ‘yan wasanta.

Tottenham ta soma yunkurin zawarcin Mourinho wanda ake yi wa lakabi da (The Special One) a turance wato Na musamman, tun lokacin da al’amura suka rikirkice wa kungiyar da kuma rashin tabuka abin a zo a gani da ‘yan wasanta ke yi tun soma kakar wasa ta bana, a karkashin mai horaswa Mauricio Pochettino, inda ko a baya-bayan nan suka sha kaye a hannun Bayern Munich da 7-2 a gasar cin kofin zakarun Turai.

Tun bayan korarsa da kungiyar Manchester United ta yi, Mourinho bai yarda ya sake kulla yarjejeniya da wata kungiya ba,

Mourinho ya sha yin watsi da tayin wasu kungiyoyin, ciki har da Benfica da kuma Lyon suka yi masa a baya-bayan nan.

Abin tambaya dai shi ne, shin ko Mourinho zai amince wa kulob din na Tottenham?

Lokaci ne kadai ke da amsar wannan tambayar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply