Ahmadu Rabe
Tsohon dan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona ya koma kungiyar Gimnasia. Maradona mai shekara 58, shi ne ya jagoran ci kungiyar kwallon kafa ta Argentina captain a lokacin da ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1986. Maradona zai horas da kungiyar ne zuwa karshen kakar wasa ta bana.
Kungiyar Gimnasia, wadda ake yi wa lakabi da sunan El Lobo, yanzu haka tana a matakin karshe ne a Lig na Primera na kasar Argentina. Kungiyar na da maki daya ne kacal a wasanni biyar da suka buga.
Maradona Wanda shi ne mai horas da kungiyar Dorados da ke Mexico ya ajiye aiki a watan Yuni saboda yana fama da rashin lafiya.
Sabon kocin na Gimnasia ya wallafa a shafinsa na Twitter: “A karshe dai komai ya tabbata, Ina matukar farin cikin kasancewa sabon kocin Gimnasia.”inji shi.
Wannan shine karo na shida Maradona yana amsar aikin horas da ‘yan wasa. Ko a baya ma ya taba horas da kungiyar kwallon kafa ta Argentina na tsawon shekara biyu daga 2008.
Maradona ya sami nasarar kai kungiyar gasar cin kofin duniya da aka yi a Afirka ta Kudu inda kuma suka kai matsayin daf da na kusa da na karshe.
Ga jerin kungiyoyin kwallon kafa da Maradona ya taba jagoranta.
Textil Mandiyu (Oct 1994 – Dec 1994)
Racing Club (Jan 1995 – Mar 1995)
Argentina (Oct 2008 – Jul 2010)
Al-Wasl (May 2011 – Jul 2012)
Al-Fujairah SC (May 2017 – Apr 2018)
Dorados (Sep 2018 – Jun 2019).
