Saleem Ashiru Mahuta
Daliban Makarantar Sakandiren Sojoji ta Nijeriya (NMS) Zaria guda 12 ne suka samu raunuka a yayin da motar da suke tafiya ta daki wani turken wutar lantarki a kan hanyar su ta Independence Road da ke cikin Kaduna.
Daliban dai na cikin kayan sojojij a cikin wata babbar mota mai cin mutane 18 mallakin Kungiyar Daliban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kadunan lokacin da abin ya faru. Nan take kuma aka kwashe wadanda suka ji rauni zuwa asibitin sojoji na mai suna 44 refrence hospital a Kaduna.
Labari mai alaka da wannan: Depot Zaria: Sojoji sun gargadi masu son shiga aikin soja
Daya daga cikin wadanda suka samu raunin ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar, su daliban makarantar sojoji ne ta Zaria kuma sun je Kwalejin Kadpoly ne a matsayin abubuwa na musamman da makarantarsu ta ware mako guda don bikin shekara-shekara. Ya ce akan hanyar su ta komawa Zaria ne tayar motar su ta fashe wanda hakan ya sa suka doki turken wutar lantarkin, sai dai kuma ya ce ba’a samu salwantar rai ba a yayin hadarin.
Saleem/dkura
