Home Coronavirus Wata ɗaya bayan Ɗangote ya bada gudunmuwar cibiyar killace masu Covid-19, har...

Wata ɗaya bayan Ɗangote ya bada gudunmuwar cibiyar killace masu Covid-19, har yanzu bata fara aiki ba

125
0

Kusan sama da wata ɗaya bayan gidauniyar Ɗangote ta sanar da bada gudunmuwar cibiyar killace masu ɗauke da Covid-19 mai gadaje 300,har yanzu ba a hannanta cibiyar ga gwamnatin jihar Kano ba.

Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta jihar Hadiza Namani ta tabbatarwa Daily Trust cewa har yanzu ana kan aikin cibiyar, kuma ko mara lafiya ɗaya ba a kwantar a ciki ba.

Aliko Ɗangote ne dai ya bada gudunmuwar cibiyar ga jihar tasa ta haihuwa.

Ya zuwa ranar Talata dai, yawan waɗanda suka kamu da cutar a jihar Kano ya kai 919, yayin da 134 suka warke 38 suka mutu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply